
Daga Najeeb Nasir
A al’adar Hausawa, ana cewa “Sara da sassaka ba ya hana gamji toho.” Wannan karin magana na nuni da cewa duk wani ƙoƙarin hana ci gaban mutum ko rage tasirinsa ba zai hana shi cimma burinsa ba matuƙar yana da jajircewa, hangen nesa da kuma sadaukarwa ga abin da yake yi.
Wannan magana ta yi daidai da irin rawar da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ke takawa a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, musamman wajen yaɗa manufofi, ayyuka da nasarorin gwamnatin ga al’umma.
Tun bayan da ya karɓi ragamar jagorancin ma’aikatar yada labarai, Waiya ya bullo da sabbin hanyoyin sadarwa da suka ƙara kusantar da gwamnati ga jama’a. Ya mayar da hankali wajen tabbatar da cewa sahihan bayanai kan shirye-shirye da ayyukan gwamnati suna isa ga al’umma cikin sauri, gaskiya da kuma fahimta.

A karkashin jagorancinsa, an samu ƙarin inganci a fannin yaɗa bayanai, inda jama’a ke samun damar fahimtar manufofin gwamnati da irin ci gaban da ake samu a fannoni daban-daban. Hakan ya taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a ga gwamnati da kuma ƙara fahimtar ayyukan da take aiwatarwa domin inganta rayuwar al’umma.
A ɓangaren harkokin cikin gida kuwa, Waiya ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai, a tsakanin al’umma. Ya jagoranci tarurruka da shirye-shirye iri daban-daban da suka haɗa da masu ruwa da tsaki, shugabannin al’umma da ƙungiyoyin fararen hula domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban al’ummar jihar.
Haka kuma, Waiya ya kasance a gaba wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin shiga harkokin dimokuraɗiyya, zaman lafiya da kuma haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma. Irin waɗannan ƙoƙari sun taimaka wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da jama’a tare da samar da kyakkyawar fahimta a tsakanin ɓangarori daban-daban.
Duk da ƙalubalen da aikin gwamnati ke tattare da shi, da kuma suke-suke da ke zuwa daga wasu ɓangarori, Waiya ya ci gaba da gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa, haƙuri da jajircewa. Maimakon ya karkata hankalinsa ga ce-ce-ku-ce, ya fi mayar da hankali wajen tabbatar da cewa muradun gwamnati da manufofinta sun isa ga jama’a yadda ya kamata.
Masu bibiyar harkokin siyasa da mulki a Kano na ganin cewa Waiya ya zama ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan gwamnatin Abba Kabir Yusuf, musamman a fagen sadarwa da hulɗa da jama’a. Sun yi imanin cewa irin ƙoƙarinsa na kare martabar gwamnati da bayyana nasarorinta ya taimaka wajen ƙarfafa fahimtar jama’a dangane da manufofin gwamnatin.
Hakika, karin maganar Hausawa ta ce “Sara da sassaka ba ya hana gamji toho.” Wannan magana na bayyana yadda duk da ƙalubale da matsin lamba, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa nasarorin gwamnatin Abba Kabir Yusuf da kuma tabbatar da cewa ayyukan gwamnati suna isa ga al’ummar Jihar Kano.
A yau, Waiya na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin amintattun Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ke aiki ba dare ba rana domin ganin an cimma manufofin gwamnatin tare da tabbatar da cewa al’ummar Kano sun amfana da dimbin shirye-shiryen ci gaba da ake aiwatarwa a jihar ya Kano.
