
Shugaban hukumar kwashe shara da kula da tsaftar muhalli na Jihar Dr. Muhammad Khalil ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai.
Dr. Muhammad Khalili ya ce hukumar na aiki da dokokin muhalli ta hanyar kafa kotun tafi-da-gidanka domin hukunta masu karya ƙa’idojin tsaftar muhalli da zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ci gaba da cewa karkashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf hukumar ta sami nasarori masu yawa da suka hada da biyan albashin ma’aikata na watanni 16 da suka rage a baya, tare da ƙara musu albashi da kuma samar musu da inshorar lafiya domin inganta walwalarsu.
Kano first

Ya kara da cewa hukumar kwashe shara ta samar da asibiti na musamman don kula da lafiyar ma’aikatanta, inda ake yi musu gwaje-gwaje da kuma kwantar da marasa lafiya idan buƙatar hakan ta taso.
Dr. Muhammad khalil ya ce hukumar ta koyawa mata sana’ar siye da siyar da shara domin su dogara da kansu.
