
…Shin akwai ma’aunin da za a iya auna Abba da Mustapha da shi?
Daga Munir Ibrahim Publisher
Ƙarfin kowace tafiyar siyasa ba ya ta’allaka ne kawai ga farin jinin jagororinta ba, face yana rataye ne a kan yadda mabiyanta ke amincewa da adalci, cancanta da bai wa kowa dama. Duk lokacin da wani mataki na siyasa ya haifar da tambayoyi game da waɗannan ƙimomi, to lallai muhawara ba za ta gaza tasowa ba.
Fito da Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC tare da Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ta haifar da tattaunawa mai faɗi a tsakanin mabiya Kwankwasiyya da kuma al’ummar Kano baki ɗaya. Dukda cewa jagororin siyasa suna da damar goyon bayan duk wanda suka ga ya dace, wannan zaɓi ya haifar da tambayoyi kan batun cancanta, gogewa da kuma makomar tsarin siyasar Kwankwasiyya.
Masu sharhi da dama sun fara kwatanta matsayin Mustapha Kwankwaso da na Gwamna Abba Kabir Yusuf. Kafin hawa kujerar gwamna, Abba Kabir Yusuf ya shafe shekaru masu yawa yana aiki a matakai daban-daban na gwamnati. Daga mukamin Mataimaki na Musamman har zuwa Kwamishina, ya samu ƙwarewa da gogewar gudanar da harkokin gwamnati. Haka kuma, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da kansa ya sha bayyana irin rawar da Abba Kabir Yusuf ya taka wajen tsarawa da aiwatar da muhimman ayyukan da aka gudanar a Kano tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015.
Kano first

A wannan mahanga ne masu suka ke cewa hujjojin da suka ba Abba Kabir Yusuf damar hawa manyan matakan jagoranci ba su bayyana a fili a wajen Mustapha Kwankwaso ba. A ganinsu, mukami mai muhimmanci kamar Mataimakin Gwamna na buƙatar gogewa a harkokin mulki, gudanarwa da kuma jagoranci.
Sai dai wannan muhawara ba ta tsaya kan mutum ɗaya ba. A zahiri, tana nuna damuwar wasu daga cikin magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya waɗanda ke ganin sadaukarwa, biyayya da dogon lokaci a cikin tafiyar na iya rasa tasirinsu wajen samun damar hawa manyan mukamai. Wannan ne ya sa ake jin ƙorafe-ƙorafe daga wasu mabiyan da ke nuna rashin gamsuwa da yadda aka yanke wannan hukunci.
A gefe guda kuma, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jawo hankalin jama’a sakamakon ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma da ake gani a sassa daban-daban na Jihar Kano. Wannan ne ya sa mutane da dama ke kallon aikinsa a matsayin wani muhimmin abin da zai yi tasiri wajen siyasar zaɓen shekarar 2027.
A ƙarshe, dorewar kowace tafiyar siyasa tana rataye ne a kan yadda shugabanninta ke gina amincewa da mabiyansu. Ko wannan muhawara za ta ƙarfafa ko kuma ta raunana tafiyar Kwankwasiyya, hakan zai dogara ne a kan yadda shugabannin tafiyar za su magance tambayoyin da suka shafi cancanta, adalci da kuma dimokuraɗiyyar cikin gida.
