
Jami’an hadin guiwa na rundunar tsaro sunyi nasarar daƙile wani hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Kanoma da ƙauyen Gidan Daji da ke garin Kanoma a Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe ranar Talata, lokacin da ‘yan bindigar ɗauke da manyan makamai suka kai farmaki kan al’ummomin yankin.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun zo da muggan makamai masu da suka haɗa da RPG, GPMG, bindigogin harbo jiragen sama da kuma AK-47. Sai dai jami’an tsaro sun samu bayanan sirri akan lokaci, lamarin da ya ba su damar kai ɗauki cikin gaggawa.
Kano first

Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, jami’an ‘yan sanda na musamman daga sashen Maru, sojojin da ke aiki a ƙarƙashin Operation Fansar Yamma, jami’an VCRU da kuma masu aikin sa-kai na yankin ne suka gwabza musayar wuta da maharan , wanda ya tilasta wa ‘yan bindigar ja da baya tare da hana su cimma manufarsu.
A yayin artabun, jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga shida da ke kan babura biyu, yayin da wasu da dama suka tsere zuwa cikin daji ɗauke da raunukan harbin bindiga. Haka kuma, ba a samu asarar rai ko jikkata ko ɗaya daga cikin jami’an tsaro ko mazauna yankunan da harin ya shafa ba. Rundunar ta ƙara tura jami’anta yankin domin ci gaba da sintiri, tabbatar da zaman lafiya da kuma farautar waɗanda suka tsere.
