
Gwamnatin jihar Borno ta ce sama da mayakan Boko Haram dubu 350 ne suka miƙa wuya tun bayan ƙaddamar da shirin gyaran hali da tunani na jihar.
Mai ba Gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Ishaq Abdullahi mai ritaya, ne ya bayyana hakan a Maiduguri yayin bikin kammala shirin gyaran hali da tunani na karo na tara.
Ya ce waɗannan mayaƙan, waɗanda suka rantse da Alƙur’ani, suna cikin rukuni na tara na waɗanda aka tantance a matsayin masu ƙarancin haɗari, kuma za a mayar da su zuwa cikin alumma su ci gaba da rayuwa.
A cewarsa, shirin na Borno ya zama ɗaya daga cikin mafi nasara a duniya wajen yaƙi da ta’addanci ta hanyoyin zaman lafiya maimakon amfani da ƙarfin soji kaɗai.
Kano first

Ishaq ya bayyana cewa tun daga shekarar 2021, shirin ya sake mayar da mayaka 8,960 cikin al’umma na rukuni takwas da suka gabata, yayin da ƙarin mutane 720 da aka kammala shirin horas da su ya kawo jimillar waɗanda aka sake tsugunarwa zuwa 9,680.
Ya ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka yiwa horan akwai mata 992 da yara 2,050 da suka miƙa wuya tare da mayaƙan.
Ya ce waɗanda suka fara fitowa daga daji sun fara kai kansu sansanin sojoji mafi kusa, inda aka yi aikin tantance su tare da karɓar makaman da suka mallaka kafin a tura su cibiyoyin gyaran hali da tunani domin horaswa.
Ya kuma ce gwamnatin jihar ta samar musu da kayan sana’o’i domin taimaka musu fara sabuwar rayuwa bayan kammala shirin.
Wadanda aka sake tsugunarwar sun fito ne daga ƙananan hukumomi da dama na jihar, da suka hada da Bama da Konduga da Maiduguri, Jere da Mafa da Dikwa da da Gwoza da Damboa da Marte da Monguno da Kukawa da Gubio da Ngala da kuma Kala Balge.
