
Abuja – Rahotanni daga majiyoyi masu kusanci da jagoran jam’iyyar NDC, Seriake Dickson, sun nuna cewa an hana wata tawaga da aka ce ta wakilci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shiga gidansa da ke Abuja domin tattaunawa kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar.
A cewar majiyar, lamarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da wakilan Kwankwaso suka isa gidan Dickson da nufin yin ganawa da shi kan sabanin da ya kunno kai game da tsarin tsayar da ‘yan takara.
Majiyar ta ce tun kafin isowar tawagar, Dickson ya bayar da umarnin kada a ba su damar shiga gidan, lamarin da ya sa suka kasa ganawa da shi.
Wannan ci gaba ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara mai zafi kan tsarin rabon takara tsakanin bangaren Kwankwasiyya da kuma bangaren tsohuwar NDC. Rahotanni sun ce ana takaddama ne kan tsarin kaso 60 cikin 100 ga bangaren Kwankwasiyya da kuma kaso 40 cikin 100 ga bangaren tsohuwar NDC.
Kano first

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan lamari na iya kara nuna irin kalubalen da ke gaban shugabannin jam’iyyar wajen samar da hadin kai da fahimtar juna tsakanin manyan bangarorin da suka hade karkashin inuwa guda.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga bangaren Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ko kuma ofishin Seriake Dickson da ke tabbatar ko musanta rahotannin.
Idan har aka tabbatar da faruwar lamarin, hakan na iya zama wata alama da ke nuna zurfafa sabanin da ke tsakanin bangarorin biyu yayin da jam’iyyar ke kokarin tsara makomarta gabanin babban zaben 2027.
