
Tsohuwar ministar harkokin jin-ƙai, Sadiya Farouq, ta roƙi babbar kotun Abuja da ta soke sammacin kama ta da aka bayar a kanta kan zargin da ake yi mata tare da wasu tsofaffin jami’an ma’aikatar.
Farouq ba ta halarci zaman kotun ranar Litinin ba, inda lauyanta ya bayyana cewa tana fama da matsalar lafiya. Sai dai lauyan EFCC ya ƙi amincewa da sauraron buƙatar, yana mai cewa ba za a iya yin hakan ba kafin a gurfanar da ita a hukumance.
Kano first

Lauyan Farouq ya dage cewa buƙatar tasa ta dace a saurare ta, domin tana neman a soke sammacin kama da kotu ta bayar a ranar 16 ga Afrilu.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie ya ɗage shari’ar zuwa ranar 10 ga Yuni domin yanke hukunci kan buƙatar da Farouq ta gabatar.