
Gwamnatin Jihar Katsina State ta dakatar da Nura Aliyu-Garwa, tsohon babban mataimaki na musamman kan ci gaban al’umma ga gwamna Dikko Radda, bayan zarginsa da aikata laifin garkuwa da mutane.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Bala Salisu-Zango ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce an dakatar da wanda ake zargin daga mukaminsa tun kafin ya nuna sha’awar tsayawa takarar ɗan majalisa.
A cewar gwamnatin jihar, Nura Aliyu-Garwa na daga cikin mutanen da ake zargi da hannu wajen sace wani yaro mai shekaru takwas a unguwar Sardauna da ke cikin birnin Katsina.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa tun da farko an dakatar da shi ne bisa zargin karkatar da kayayyakin tallafawa al’umma da aka ware wa ƙaramar hukumar Batsari a ƙarƙashin shirin ci gaban al’umma na jihar.
Hukumomin jihar sun ce za su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin gudanar da bincike kan lamarin.
