
Wannan na zuwa yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Amman, inda Ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro na Najeriya, Bello Matawalle, da Shugaban Hafsoshin Sojin Jordan, Yousef A. Alhnaity suka halarta.
Yarjejeniyar na da manufar inganta haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu a fannoni da suka haɗa da yaƙi da ta’addanci, horar da jami’an tsaro, binciken harkokin tsaro da kuma musayar bayanan sirri.
Haka kuma, ɓangarorin biyu sun amince da ƙara haɗin gwiwa wajen bunƙasa fasahar tsaro da kafa hanyoyin musayar ƙwarewa tsakanin sojojin ƙasashen.
Ministan ya bayyana yarjejeniyar a matsayin muhimmiyar dama da za ta ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Jordan, musamman a wannan lokaci da ƙalubalen tsaro ke ƙaruwa a duniya.
Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankuna daban daban.
