
Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta sake bayar da sammacin kama tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, bayan ya kasa gurfana a gaban kotu a yau ranar Litinin din nan
Wannan ne karo na biyu cikin mako guda da kotun ke bayar da umarnin kama tsohon ministan saboda rashin halartar zaman shari’a.
Rahotanni sun nuna cewa kotun ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da ci gaba da shari’ar da ake yi masa.
