Wannan albishir da gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf yayi ga maniyata yana fitowa a cikin jawaban Mataimakin gwamnan jihar kano Alh Murtala Sule Garo a wajen taron gwajin aikin Hajji da aka gabatar wa a filin masaukin Alhazai na jihar kano.
Mataimakin gwamnan ya ja kunnen maniyatan da su sani tafiya aikin Hajji ba tafiya yawon buda idanu ba ne, tafiyar ibada ce kuma mai tsaki wadda take bukatar tsantsar natsuwa da biyayya ga Allah dan haka ne ma ake gabatar muku da gwajin aikin
Haka ya Kara Kiran maniyatan da su zama jakadu na gari a Kasa mai tsarki.
Mai Martaba Sarki Gaya Alh Aliyu Ibrahim Abubakar ya yi kira gare su da su zama masu hakuri da juna a kasa Mai tsarki.
Shugaban shirya na Arewa masu yamma Alh Umar Muhd Kalgo a jawabinsa yace yayi shekaru a wannan mukami amma baiga shiri irin na jahar Kano ba
Daga karshe babban darakta Hukumar alhazai ta jihar kano ya tabbatar an yiwa maniyata aikin Ha

