
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta wallafa a Shafinta na internet cewa tana neman tsohowar ministar jin ƙai ta ƙasa Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo
Sanarwar ta ce tana neman tsohuwar ministar bisa zarge zargen laifukan haɗa baki domin aikata laifuka da amfani da ofishi ba bisa ƙa’ida ba da karkatar da kuɗin gwamnati alokacin datake kan mukaminta
Sanarwar EFCCn ta buƙaci jama’a su sanar da hukumar duk inda suka ga tsohuwar ministan domin kama ta.
Sadiya Umar Farouq dai itace tsohuwar ministar jin ƙai a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar, marigayi Muhammadu Buhari.
