
By Mutawakkilu Ibrahim Idris
Wasu ‘yan bindiga sun sace aƙalla ɗaliban dake shirin rubuta jarabawar shiga jami’a wato (JAMB) guda 14 tare da wasu matafiya a wani hari da suka kai kan motar bas a jihar Benue.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne akan hanyar Makurdi zuwa Otukpo, lokacin da maharan suka tare motar bas ɗin da ke ɗauke da fasinjoji, suka kuma yi awon gaba da mafi yawansu zuwa cikin daji.
An ce motar na ɗauke da kusan mutane 18, inda yawancinsu matasa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa rubuta jarabawar JAMB da ake shirin farawa ranar Juma’a da kuma Asabar.
Sai dai mutum daya ne kacal ya samu nasarar tserewa daga hannun maharan.
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa jami’anta sun fara bincike tare da ɗaukar matakan ceto waɗanda aka sace.
Al’amarin ya sake jaddada matsalar tsaro da ke addabar wasu yankunan ƙasar, musamman yadda yake shafar matasa da harkar ilimi.
