Comishinan Yada Labarai na Kano Ya Halarci Taron Kungiyar Masu Sauraron Rediyo

Daga: Mutawakkilu Ibrahim Idris
Comishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya halarci taron kungiyar masu sauraron rediyo ta jihar Kano, inda ya jaddada muhimmancin rawar da rediyo ke takawa wajen wayar da kan al’umma, musamman matasa.
A yayin taron, Waiya ya yabawa mambobin kungiyar bisa kokarinsu na ilmantar da matasa kan muhimmancin sauraron rediyo tare da yin tsokaci mai ma’ana kan abubuwan da suke saurara. Ya bayyana cewa wannan mataki na taimakawa wajen gina al’umma mai ilimi da fahimta.
Haka kuma, ya kara musu kwarin gwiwa tare da tabbatar musu da cewa ofishinsa a shirye yake domin tallafa wa kungiyar, musamman wajen bunkasa ayyukansu da inganta ci gabanta.
A karshe, Comishinan ya bukaci shugabannin kungiyar da su gabatar da sunayen mutane biyar daga cikin mambobinsu, domin a ba su tallafin jari na kasuwancin POS, a matsayin wata hanya ta karfafa tattalin arzikinsu.