
Gwamnatin Jihar Kano ta umarci Jami’ar Azman da ke Kano da ta gabatar wa Kwamitin Gwamnati Mai Yaki da Gini Ba Bisa Ka’ida Ba dukkan takardun da suka shafi mallakar ƙasa da izinin gine-ginen da ke harabar jami’ar, ko kuma ta fuskanci matakin rufe makarantar.
Shugaban kwamitin kuma Babban Daraktan Hukumar Kula da Tsare-tsaren Filaye ta Jihar Kano (KANGIS), Dakta Dalhatu Aliyu Sani, ne ya bayyana hakan yayin wani rangadi da kwamitin ya gudanar.
Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na gano da kuma dakatar da gine-gine da ayyukan kasuwanci da ake gudanarwa ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba a faɗin jihar Kano.

Dakta Dalhatu ya buƙaci shugabannin Jami’ar Azman da sauran cibiyoyin da kwamitin ya ɗauki mataki a kansu da su gabatar da takardun mallakar ƙasa, izinin gini da sauran muhimman takardu da hukumomin da abin ya shafa suka bayar.
Ya gargadi cewa duk wata hukuma ko cibiya da ta gaza bin umarnin gwamnati za ta iya fuskantar ƙarin matakan doka, ciki har da rufe wuraren da abin ya shafa.
A wani ɓangaren kuma, kwamitin ya sanar da kulle gidan man fetur na Azman da ke cikin harabar jami’ar, bisa zargin karya dokokin tsara birane da amfani da ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaban kwamitin ya jaddada cewa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta himmatu wajen tabbatar da bin doka, inganta muhalli da kuma dawo da tsarin birane a ƙarƙashin manufar “Kano First”.
Haka kuma, ya ce kwamitin na ci gaba da karɓar korafe-korafen jama’a kan gine-ginen da suka toshe hanyoyin ruwa ko kuma suke karya dokokin tsara birane domin ɗaukar matakan da suka dace.
