
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kalubalanci Gwamnatin Jihar Kano da ta gabatar da hujjoji masu inganci kan zargin cewa ya karɓi wasu kuɗaɗen kananan hukumomi ta hannun ɗansa, Mujahid Aminu Abdussalam.
Kalubalen na Gwarzo ya biyo bayan zargin da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi cewa an rika tura wasu kuɗaɗen kananan hukumomi zuwa ga tsohon mataimakin gwamnan ta hannun ɗansa.
Kano first

A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar a ranar Alhamis, Gwarzo ya bayyana zargin a matsayin mara tushe, yana mai cewa an yi shi ne domin bata masa suna a idon jama’a.
Sanarwar ta ce babu wata hujja ko sahihin tushe da ke goyon bayan zargin, tare da ƙalubalantar masu yin zargin da su fito da cikakkun hujjoji da za su tabbatar da ikirarinsu.
Gwarzo ya jaddada cewa a duk tsawon lokacin da ya yi a harkokin gwamnati ya kasance mai bin doka, gaskiya da riƙon amana, yana mai ƙara da cewa bai taɓa shiga wani lamari da ya saɓa wa ƙa’idojin aiki ba.
Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar cewa gaskiya za ta bayyana a ƙarshe, tare da kira ga al’umma da su yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin zarge-zargen da ba su da tushe ko makama.
