
Gwamnatin Kano ta kafa wani kwamitin bincike da zai gano yadda ake sace tare siyar da gyadar tamowa wacce gwamnatin jiha ta samar domin yara masu cutar yunwa.
Da yake ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce an kafa kwamitin ne domin binciko yadda ake karkatar da kayayyakin da kuma tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki.
Kano first

Dakta Abubakar Labaran ya ce aikin kwamitin shi ne binciken yadda aka karkatar da kayayyakin da gano mutanen da ke da hannu a lamarin, ciki har da ma’aikatan lafiya da ’yan kasuwa .
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da naira miliyan 500 wajen siyo kayayyakin domin kula da yara masu fama da cutar tamowa.
Babban sakatare a ma’aikatar Lafiya ta Jiha Pharmacist Aminu Bashir, ne shugaban kwamitin, da ya ƙunshi mambobi 18 da suka hada da jami’an tsaro da wakilan masarautu da kwamitocin ci gaban unguwanni.
An bawa kwamitin makwanni biyu da ya kawo rahotonsa
