
Shugabannin Ƙungiyar Kansilolin Jihar Kano sun kai ziyara ga Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, inda suka bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban ƙungiyar, Kwamared Kabir Marakas Dala, wanda shi ne Kansilan Kantudu, ya jagoranci tawagar zuwa ziyarar, inda ya bayyana cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar shugabannin da suke goyon baya.
Ya ce ƙungiyar ta nuna goyon baya dari bisa dari ga jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa la’akari da ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma da gwamnatinsa ke aiwatarwa a sassa daban-daban na Jihar Kano.
Da yake mayar da jawabi, Kwamishina Ibrahim Abdullahi Waiya ya tabbatar wa shugabannin ƙungiyar cewa zai ci gaba da ba su goyon baya wajen tunkarar batutuwan da suka shafi kansiloli da kuma isar da matsalolinsu ga mahukunta, musamman Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan ya kuma yaba wa shugabannin ƙungiyar bisa zaɓar ofishinsa a matsayin wurin da suka fara kai ziyarar, yana mai cewa hakan alama ce ta ƙauna da amincewa.
A ƙarshe, Kwamared Waiya ya yi wa shugabannin ƙungiyar fatan alheri, nasara da ci gaba mai ɗorewa a ayyukansu, tare da tabbatar musu da shirinsa na ci gaba da haɗin gwiwa da su domin cimma muradun al’umma.
