
Babbar Kotun Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Farida Dan Baffa, ta yanke wa Shuaibu Abdulkadir, mazaunin unguwar Farawa a Ƙaramar Hukumar Kumbotso, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe Rumaisa Shuaibu mai shekaru 22.
Kotun ta bayyana cewa hujjojin da aka gabatar sun tabbatar ba tare da wata shakka ba cewa wanda aka yankewa hukuncin ya aikata laifin kisan bayan marigayiyar ta ɗauki ciki daga gare shi.
An gurfanar da Shuaibu Abdulkadir a ranar 23 ga Agustan 2025 bisa zargin kisan kai, laifin da Sashe na 221 na Dokar Penal Code ya tanadi hukuncin kisa a kansa.

A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu uku tare da hujjoji da suka haɗa da bidiyon yadda aka aikata laifin, bayanan furuci da wanda aka yankewa hukuncin ya rubuta, hotunan mamaciyar, wuƙar da aka yi amfani da ita wajen kisan da kuma wayarsa ta hannu.
Bayan nazarin hujjojin da aka gabatar, kotun ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wanda aka samu da laifin.
Da yake martani kan hukuncin, Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya bayyana cewa hukuncin ya nuna ƙudirin gwamnatin jihar na tabbatar da adalci, kare haƙƙin waɗanda aka zalunta da kuma hukunta masu aikata manyan laifuffuka. Haka kuma ya yabawa lauyan gwamnati, Barr. Basiru Kabiru Aliyu, saboda ƙwarewa da jajircewarsa wajen gudanar da shari’ar.
Brown Pigeon News za ta ci gaba da bibiyar manyan labarai tare da kawo muku sahihan bayanai cikin gaggawa.
