
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro domin kare dimokuraɗiyya da martabar ƙasa.
Da yake jawabi a taron ƙasa kan tsaro da ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya a Abuja, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya isar da saƙon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda ya bayyana muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen wayar da kan jama’a da tallata manufofin gwamnati.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa wajen isar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati ga matasa da sauran al’umma, tare da jaddada alhakin ‘yan jarida na yaƙi da yaɗa labaran ƙarya, bayanan da ba su da tushe da kuma yaudarar jama’a.
“Kafofin yaɗa labarai suna da alhakin sanar da jama’a ayyukan gwamnati tare da kare martaba da haɗin kan ƙasa. Wannan wani bangare ne na nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mana a matsayin ‘yan ƙasa,” in ji Waiya.

Kwamishinan ya yabawa taken taron, wanda ya mayar da hankali kan alaƙar da ke tsakanin tsaro da aikin jarida, yana mai cewa taken ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar haɗin kai tsakanin bangarorin biyu.
Ya ƙara da cewa rahotannin da suka shafi tsaro na buƙatar taka-tsantsan da ƙwarewa, inda ya bukaci kafofin yaɗa labarai su daidaita tsakanin ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma kare muradun ƙasa.
Waiya ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta ci gaba da kyakkyawar alaƙa da hukumomin tsaro, inda take ba su tallafi na kayan aiki da motocin gudanar da aiki ga Rundunar ‘Yan Sanda, NSCDC, JTF da sauran hukumomin tsaro domin inganta ayyukansu.
Ya kuma tabbatar da cewa kafafen yaɗa labarai na gwamnati da masu zaman kansu a Kano na aiki cikin yanayi mai ‘yanci ba tare da tsangwama ko razana ba. Haka kuma gwamnati na shirya horaswa da tarurrukan ƙara wa ‘yan jarida ƙwarewa lokaci zuwa lokaci domin bunƙasa aikin jarida.
“Muna gina kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati, kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro. Tallafa wa jami’an tsaro ba wai taimaka musu kawai ba ne, har ma kariya ce gare mu a matsayin al’umma,” in ji shi.
A ƙarshe, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sake tabbatar da jajircewar gwamnatin Kano wajen mutunta kundin tsarin mulki, kare ‘yancin aikin jarida da kuma inganta shugabanci na haɗin gwiwa, yana mai cewa haɗin kai tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa.
