
Kungiyar Coalition for Accountability and National Development (CAND) ta yi kira ga hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci da rashawa da su fadada binciken da suke yi kan wani kaso na danyen zinariya mai nauyin kilogram 22.2, wanda darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 4.4, da Hukumar EFCC ta kama a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC na shiyyar Kano sun kama wani jami’in Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA), Anas Baffa, bisa zargin boye danyen zinariyar a cikin wandonsa domin tsallake binciken tsaro kafin a mika ta ga wasu fasinjoji da ke shirin fita kasashen waje.
Kungiyar CAND ta bayyana cewa ya zama dole hukumomi su zurfafa bincike kan safarar zinariya ba bisa ka’ida ba da kuma ayyukan hakar ma’adinai da ke gudana ba tare da bin dokoki ba. A cewar daraktan kungiyar, Ibrahim Musa, irin wadannan ayyuka na hana gwamnati samun kudaden shiga tare da kara rura matsalolin tsaro a wasu sassan kasar nan.
Kungiyar ta kuma bukaci a binciki wasu fitattun mutane da ake dangantawa da harkar ma’adinai, ciki har da tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, EFCC ba ta bayyana Sanata Abdulaziz Yari a matsayin wanda ake zargi a binciken da ake gudanarwa ba, kuma babu wata sanarwa daga hukumar da ke danganta shi kai tsaye da lamarin.
Kano first

A wani bangare kuma, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Junaidu Aminu, ya yi ikirarin a wani bidiyo da ya wallafa a TikTok cewa jami’an bincike suna gudanar da bincike kan wani jirgin Ethiopian Airlines a filin jirgin saman Kano.
Ya ce masu binciken sun gano akwatuna 15 da ake zargin an boye bayanansu, tare da ikirarin cewa suna dauke da wasu kayayyaki masu hadari. Duk da haka, babu wata hukuma da ta tabbatar da wannan ikirari a hukumance.
Junaidu ya kuma yi zargin cewa hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba na da alaka da matsalolin tsaro kamar garkuwa da mutane da ayyukan ‘yan bindiga a Arewacin Najeriya, musamman a jihar Zamfara.
Haka kuma, wata kungiyar farar hula mai suna “Mai Kare Talakawa” da ke jihar Sokoto ta bukaci a yi karin haske kan asalin wasu manyan kadarorin Sanata Yari.
Rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta nuna damuwa kan yadda kamfanin MA’AM Energy Limited ya samu kaso 95 cikin 100 na hannayen jarin Geregu Power Plc daga fitaccen dan kasuwa Femi Otedola a watan Disamban 2025, a wata yarjejeniya da aka kiyasta kudinta ya haura Naira tiriliyan 1.08.
Duk da haka, babu wata hukuma da ta tabbatar da wata alaka tsakanin wannan cinikin kasuwanci da binciken safarar zinariyar da EFCC ke yi. Haka kuma, Sanata Abdulaziz Yari bai fitar da wata sanarwa kai tsaye ba kan zarge-zargen da kungiyoyi da masu sharhi suka yi masa.
Brown Pigeon News na ci gaba da bibiyar wannan lamari tare da jiran karin bayanai daga EFCC da sauran hukumomin da abin ya shafa.
