Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Business
  • Education
  • Featured
  • Health
  • Politics
  • Sports
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram
Facebook Instagram TikTok
BROWN PIGEON MEDIA
SUBSCRIBE
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    FEDERAL GOVERNMENT SUSPENDS PROPOSED WAEC, NECO REGISTRATION FEE HIKE

    July 13, 2026

    FG: FANNIN MA’ADANAI YA JAWO JARIN DALA BILIYAN 3 CIKIN SHEKARU UKU

    June 18, 2026

    GWAMNATIN TARRAYYA TA MUSANTA SHIRIN SOKE HUKUMAR NBAIS

    June 18, 2026

    DEMOCRACY DAY SPEECH: OUR GENERATION MUST SECURE PROSPERITY 

    June 12, 2026

    Senator Barau Reaffirms ECOWAS Parliament’s Commitment to Regional Unity at Commissioning of New ECOWAS Headquarters

    July 3, 2026

    DA DUMI-DUMI: Starmer ya yi Murabus Daga Mukamin Firaministan Birtaniya

    June 22, 2026

    NETANYAHU YA SHA ALWASHIN HANA IRAN MALLAKAR MAKAMIN NUKILIYA

    June 13, 2026

    Girgizar Ƙasa Mai Ƙarfi Ta Hallaka Mutane a Philippines, Ana Fargabar Tsunami a Wasu Ƙasashe

    June 8, 2026

    WAIYA PLEDGES COLLABORATION WITH EX-COUNCILLORS’ FORUM, NORTH WEST APC WOMEN MEDIA GROUP AS BOTH DECLARE SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA

    August 4, 2026

    Ibrahim Abdullahi Waiya: Leadership Defined by Focus, Vision and Service

    August 4, 2026

    KANO RECORDS REVENUE SURGE AS DIGITAL LAND SYSTEM RAISES MONTHLY EARNINGS TO ₦750 MILLION

    August 3, 2026

    Waiya Reaffirms Kano Government’s Commitment to Community-Led Security, Peacebuilding

    August 3, 2026
  • Business

    KASEDA TA GUDANAR DA SHIRIN WAYAR DA KAI GA MSMEs KAN KA’IDOJIN NAFDAC A JIHAR KATSINA

    June 12, 2026

    Dangote Industrialising Africa– NCCIMA DG

    May 17, 2026

    INEC TA BUKACI MASU RIJISTAR KATIN ZABE A KANO DA SU JE SU DUBA SUNAYENSU

    April 27, 2026

    KANO TO HOST NATIONAL LAUNCH OF ECoN INITIATIVE, SET TO DRIVE INNOVATION AND INDUSTRIAL GROWTH IN NORTH-WEST

    April 16, 2026

    NewsNigeria’s Inflation Rate Climbs to 15.38% in March

    April 16, 2026
  • Education

    KANO PRIVATE SCHOOLS BOARD SUSPENDS 10% STATUTORY TAX PENDING FRESH ASSESSMENT

    August 1, 2026

    2027 PRESIDENCY: TINUBU DECLARES UNIVERSITY DEGREE, LEAVES OUT PRIMARY, SECONDARY EDUCATION

    August 1, 2026

    Governor Abba Kabir Yusuf, Education Minister Commission New Girls’ Secondary School in Kumbotso

    July 22, 2026

    Gwamnatin Kano Ta Umarci Jami’ar Azman Ta Gabatar da Takardun Gini Ko Ta Fuskanci Rufe Makarantar

    June 23, 2026

    Kano Govt Reaffirms Commitment to Children’s Welfare at International Children’s Day Celebration

    June 14, 2026
  • Featured

    Kano State Government Organises Two-Day Retreat for Online Media Publishers in Jigawa

    January 15, 2026

    Former Kano APC Councilors Hold Special Prayers for Governor Abba Kabir Yusuf

    October 27, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    Kano Government Clarifies Position on Elders Council, Backs Its Own Initiative

    September 7, 2025
  • Health

    NORTH-WEST DEVELOPMENT COMMISSION TEAMS UP WITH DALA ORTHOPAEDIC HOSPITAL TO EASE MEDICAL COSTS

    August 1, 2026

    Kano Government Targets Maternal Mortality with 484 New Mini-Ambulances for Rural Wards

    June 19, 2026

    Gwamnatin Kano Ta Sayi Ƙananan Motocin Asibiti 484 Domin Taimaka wa Mata Masu Juna Biyu – Kwamishinan Lafiya

    June 19, 2026

    SHAYAR DA NONON UWA ZALLA NA KARE YARA DAGA CUTUTTUKA — KWAMISHINAN LAFIYA

    June 16, 2026

    Hukumar Kula da Asibitocin Kano Ta Tsaurara Matakai Kan Rashin Zuwa Aiki bisa Jadawalin Ayyuka

    June 11, 2026
  • Politics

    SANATA RUFAI SANI HANGA YA FICE DAGA JAM’IYYAR NDC

    August 3, 2026

    KWANKWASIYYA-SHEKARAU UNITY FORUM REBRANDS, DECLARES TOTAL SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA KABIR YUSUF AHEAD OF 2027

    July 21, 2026

    Governor Abba Kabir Yusuf Declares Murtala Sule Garo as 2027 Deputy Governorship Running Mate

    July 13, 2026

    APC zata Bayyana Shettima a Matsayin Mataimakin Takarar Tinubu na 2027

    July 10, 2026

    TSOFAFFIN SHUGABANNIN ƘANANAN HUKUMOMI DA KANSILOLI SUN BAYYANA GOYON BAYANSU GA GWAMNA ABBA KABIR YUSUF

    July 10, 2026
  • Sports

    Bichi First FC Unveils Abubakar Senior as New Technical Adviser

    September 11, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    If Super Eagles Fail to Qualify for World Cup, Nigerians Will Not Forgive Us – Ahmed Musa

    September 6, 2025

    Super Falcons striker and six-time African Women’s Footballer of the Year, Asisat Oshoala, has completed her move from Bay FC to Saudi Women’s Premier League side Al Hilal

    September 3, 2025
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
BROWN PIGEON MEDIA
Home » SULHU DA MASU RAJIN RABA ƘASA: HANYAR ZAMAN LAFIYA KO BARAZANA GA DOKA?
News

SULHU DA MASU RAJIN RABA ƘASA: HANYAR ZAMAN LAFIYA KO BARAZANA GA DOKA?

Brown Pigeon MediaBy Brown Pigeon MediaJune 14, 20265 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp Telegram Email Copy Link
Mutawakkilu Ibrahim Idris
SULHU DA MASU RAJIN RABA ƘASA: HANYAR ZAMAN LAFIYA KO BARAZANA GA DOKA?

 

Mutawakkilu Ibrahim Idris
SULHU DA MASU RAJIN RABA ƘASA: HANYAR ZAMAN LAFIYA KO BARAZANA GA DOKA?

Tattaunawa Ko Rage Tashin Hankali? Dalilin da Ya Sa Yin Sulhu da Shugabannin Ƙungiyoyin Masu Rajin Raba Ƙasa da Aka Yanke Wa Hukunci Zai Iya Raunana Ƙarfin Hana Laifi na Ƙasa

 

Daga Mohammed Babagana Abubakar

 

A duk lokacin da ake tattaunawa kan sasanta rikice rikicen ƙasa da samar da haɗin kai, ana yawan ganin cewa yin sulhu da masu korafi ko masu tayar da hankali ita ce hanya mafi sauri ta samun zaman lafiya. A lokucin da ƙasa ke fuskantar matsalolin tsaro da sabanin ra’ayoyin yankuna daban daban, wasu shugabanni kan ga cewa yin sassauci da tattaunawa da waɗannan ƙungiyoyi zai taimaka wajen rage tashin hankali da dawo da kwanciyar hankali.

 

Duk da cewa tattaunawa muhimmiyar hanya ce ta warware rikice rikice, tana zama abin damuwa idan har ta fara maye gurbin tsarin shari’a da kuma ka’idar ɗaukar alhakin laifuffuka. Wannan muhawara ta sake tasowa bayan kalaman tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, a wani taron tattaunawa da aka gudanar a birnin Washington D.C., inda aka ruwaito cewa ya bayyana cewa babu wani dalili mai ƙarfi da zai sa a ci gaba da tsare shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, tare da jaddada cewa tattaunawa ce mafita ga rikicin yankin Kudu maso Gabas.

 

Masu goyon bayan irin wannan matsayi suna ganin cewa tattaunawa za ta taimaka wajen magance korafe korafen da ke haddasa rikice rikice tare da ƙarfafa haɗin kan ƙasa. Sai dai masu suka suna ganin cewa duk wani yunƙuri na kawar da hukuncin kotu ko kauce wa sakamakon shari’a ta hanyar siyasa na iya raunana ginshiƙin doka da oda tare da haifar da matsalolin tsaro a nan gaba.

 

Babban abin da ake tattaunawa a kai shi ne bambanci tsakanin yancin faɗar albarkacin baki da kuma ɗaukar alhakin laifuffuka. Duk da cewa rashin gamsuwa da gwamnati da bayyana ra’ayi na siyasa haƙƙi ne a tsarin dimokuraɗiyya, gwamnatin Najeriya ta dage cewa batun Nnamdi Kanu ya wuce maganganun siyasa kawai. Bayan shekaru na shari’a, wata Babbar Kotun Tarayya ta yanke masa hukunci a shekarar 2025 kan manyan laifuffuka da suka shafi tsaro tare da ɗaure shi har abada.

 

Ko da kuwa mutum yana goyon baya ko adawa da wannan hukunci, tambayar da ya kamata a yi ita ce. Wane saƙo ne gwamnati ke aikawa idan ta nuna shirinta na sauya sakamakon shari’a ta hanyar sulhun siyasa?

Kano first

Mutawakkilu Ibrahim Idris

Daya daga cikin muhimman ayyukan kowace ƙasa mai cikakken iko shi ne tabbatar da cewa ita kaɗai ce ke da ikon amfani da ƙarfi bisa doka da kuma gudanar da adalci. Kotuna an kafa su ne domin tantance gaskiya da yanke hukunci bisa hujjoji da dokoki. Idan aka bari siyasa ta rinjayi hukuncin kotu, amincewar jama’a ga tsarin shari’a da yancin kotuna na iya fara raguwa.

 

Wannan batu bai tsaya kan mutum guda ba. Masana harkokin tsaro suna gargadin abin da ake kira moral hazard, wato yanayin da bayar da lada ko sassauci ga wani hali zai iya ƙarfafa wasu su ma su aikata irin wannan abu. Idan ƙungiyoyi suka fahimci cewa tashin hankali ko ƙalubalantar gwamnati na iya haifar musu da sassauci ko afuwa daga gwamnati, hakan na iya sa wasu su ɗauki irin wannan hanya domin cimma burinsu.

 

A irin wannan yanayi, masu bin hanyoyin lumana wajen neman sauyi za su iya ganin cewa dabarunsu ba sa haifar da sakamako kamar yadda tashin hankali ke yi. Wannan na iya haifar da mummunan al’ada inda wasu ke ganin cewa hanya mafi sauri ta jawo hankalin gwamnati ita ce tayar da rikici maimakon amfani da hanyoyin da kundin tsarin mulki ya tanada.

 

Haka kuma akwai batun sadaukarwar jami’an tsaro da hukumomin tabbatar da doka. Yaƙi da ta’addanci da gudanar da bincike kan manyan laifuffuka na buƙatar lokaci, kuɗi da sadaukarwa mai yawa. Jami’an tsaro da dama suna fuskantar haɗari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

 

Idan bayan irin wannan ƙoƙari aka juya aka mayar da hukuncin kotu wani batu na ciniki a siyasa, hakan na iya rage ƙwarin gwiwar jami’an tsaro. Za su iya fara tambayar ko ƙoƙarinsu zai kasance mai amfani idan daga ƙarshe za a iya sauya sakamakon ta hanyar siyasa.

 

Wannan ba yana nufin cewa tattaunawa ba ta da muhimmanci ba. A’a, tarihi ya nuna cewa tattaunawa mai ma’ana na iya taimakawa wajen rage rikice rikice da samar da fahimtar juna. Amma mafi ingancin tattaunawa ita ce wadda ke aiki tare da tsarin doka, ba wadda take maye gurbinsa ba.

 

Al’umma mai bin tsarin dimokuraɗiyya dole ne ta daidaita tsakanin sulhu da kuma tabbatar da adalci. Zaman lafiya na gaskiya ba ya samuwa ne kawai ta hanyar yin sassauci na siyasa, sai dai ta hanyar ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, tabbatar da adalci ga kowa da kuma gina amincewar jama’a cewa doka ba ta nuna son kai kuma ba abin ciniki ba ce.

 

Najeriya na fuskantar ƙalubalen tsaro masu yawa waɗanda ke buƙatar hikima da tsayin daka. Yayin da ake ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da magance korafe korafen yankuna, dole ne a yi hakan cikin iyakokin kundin tsarin mulki da doka.

 

A ƙarshe, ƙarfin dimokuraɗiyya yana bayyana ne ba ta yadda take sassauta doka saboda matsin lambar siyasa ba, sai dai ta yadda take tsayawa kan ka’idojin adalci ko da lokacin da hakan ba zai kawo ribar siyasa ba. Idan Najeriya na son tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kuma hana tashe tashen hankula a nan gaba, wajibi ne a ci gaba da mutunta doka da hukuncin kotuna. Tattaunawa tana da muhimmanci, amma adalci dole ne ya kasance shi ne kalma ta ƙarshe.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email VKontakte WhatsApp Copy Link
Previous ArticleSETTING THE SENATE ABLAZE WITH PERFORMANCE: BARAU JIBRIN’S HISTORIC 42-BILL MASTERPIECE
Next Article Dialogue or De-escalation? Why Negotiating Convicted Separatist Leaders Could Undermine National Deterrence

Related Posts

WAIYA PLEDGES COLLABORATION WITH EX-COUNCILLORS’ FORUM, NORTH WEST APC WOMEN MEDIA GROUP AS BOTH DECLARE SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA

August 4, 2026

Ibrahim Abdullahi Waiya: Leadership Defined by Focus, Vision and Service

August 4, 2026

KANO RECORDS REVENUE SURGE AS DIGITAL LAND SYSTEM RAISES MONTHLY EARNINGS TO ₦750 MILLION

August 3, 2026

Waiya Reaffirms Kano Government’s Commitment to Community-Led Security, Peacebuilding

August 3, 2026

WAIYA YA JADDADA MUHIMMANCIN HAƊIN GWIWA TSAKANIN AL’UMMA DA GWAMNATI WAJEN INGANTA TSARO A JIHAR KANO

August 3, 2026

Kosan Waka Dies at 47 as Gov. Yusuf Mourns Renowned Political Singer

August 2, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Stay In Touch
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • Telegram
  • WhatsApp
Latest Posts

WAIYA PLEDGES COLLABORATION WITH EX-COUNCILLORS’ FORUM, NORTH WEST APC WOMEN MEDIA GROUP AS BOTH DECLARE SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA

By Brown Pigeon MediaAugust 4, 2026

The Kano State Commissioner of Information and Internal Affairs, Comrade Ibrahim Abdullahi…

Ibrahim Abdullahi Waiya: Leadership Defined by Focus, Vision and Service

August 4, 2026

KANO RECORDS REVENUE SURGE AS DIGITAL LAND SYSTEM RAISES MONTHLY EARNINGS TO ₦750 MILLION

August 3, 2026

SANATA RUFAI SANI HANGA YA FICE DAGA JAM’IYYAR NDC

August 3, 2026

Waiya Reaffirms Kano Government’s Commitment to Community-Led Security, Peacebuilding

August 3, 2026
© 2026 Brown Pigeon Media. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.