
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta ta yin aiki tare da gwamnatocin jihohi, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai domin gina ingantaccen tsarin kariyar zamantakewa da zai taimaka wajen rage talauci a Najeriya. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana haka a taron tattaunawar manufofi na yankin Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kano, inda ya ce kariyar zamantakewa na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da cewa talakan Najeriya ya samu saukin rayuwa
Shettima ya bayyana cewa akwai buƙatar Najeriya ta wuce tsarin taimako na wucin gadi zuwa kafa ɗorewar tsare-tsare masu inganci don dogaro da kai Ya yabawa muhimmancin yankin Arewa maso Yamma ga tattalin arzikin ƙasa, se dai ya nuna damuwa kan matsalolin da yankin ke fuskanta kamar talauci, ƙarancin ilimi da lafiya, yawan mace-macen mata masu juna biyu, rashin abinci mai gina jiki ga yara, da kuma matsalar yara da ba sa zuwa makaranta.
Kano first

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Dandalin Gwamnonin Arewa maso Yamma, Dikko Umaru Radda, ya ce rage talauci zuba jari ne ga makomar yankin. Haka kuma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jaddada muhimmancin tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun kai ga inganta rayuwar jama’a, musamman mata, yara, matasa da masu nakasa. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta ce tsarin kariyar zamantakewa na taimakawa al’umma su jure matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da sauyin yanayi.
Har ila yau, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Shirye-shiryen Ci Gaban Yankuna, Mariam Temitope Masha, ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ware shekarar 2026 a matsayin Shekarar Iyali da Kariyar Zamantakewa. Mahalarta taron sun amince cewa haɗin gwiwa tsakanin jihohi, samar da ɗorewar hanyoyin samun kuɗi da kuma aiwatar da shirye-shiryen kariyar zamantakewa cikin tsari su ne hanyoyin rage talauci da inganta rayuwar miliyoyin mutane a yankin Arewa maso Yamma. Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ciki har da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
