
An zargi ICPC da hana Nasir El-Rufai ganin likita duk da matsalar da ake zargin tana damunsa a idanunsa yayin tsarewa.
Mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce El-Rufai ya nemi kulawar lafiya amma ba a ba shi damar zuwa asibiti ba.
Har yanzu ICPC ba ta fitar da wata sanarwa kan zargin ba.
Shin duk wanda ake tsare da shi bai kamata ya samu kulawar lafiya ba? Ku bayyana ra’ayoyinku.
