
Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta bayyana ƙwarin gwiwarta cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi nasara wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a Najeriya.
Ta ce gwamnatin Tinubu na aiki ba dare ba rana domin magance matsalolin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.
Remi ta buƙaci ‘yan Najeriya su ci gaba da haƙuri da goyon baya, tana mai cewa shugaban ƙasar zai murƙushe ƙungiyoyin masu laifi tare da samar da ingantaccen tsaro.
