
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma jigo a jam’iyyar ADC, Babachir David Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar bayan kammala zabukan fidda gwani na cikin gida.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Lawal ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne sakamakon abin da ya kira rashin adalci da kuma magudin da aka yi a yayin gudanar da zabukan fidda gwani.
Ya zargi shugabannin jam’iyyar da murde tsarin zaɓen domin fifita tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, tare da bai wa magoya bayansa gata a matakai daban-daban na zaɓen.
Lawal ya ce zabukan fidda gwanin da aka gudanar sun kasance cike da kura-kurai da zarge-zargen sauya sakamako, lamarin da ya ce ya saɓa wa manufofin dimokuraɗiyya da adalci da jam’iyyar ke ikirarin tsayawa a kai.
Ya ƙara da cewa ba zai ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar da ke kauce wa gaskiya da adalci ba, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da fafutukar ganin an samar da shugabanci nagari da gaskiya a siyasar Nijeriya.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, shugabannin jam’iyyar ADC ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan zarge-zargen da Babachir Lawal ya yi ba.
