
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da haɗa Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Muhalli da Sauyin Yanayi zuwa ma’aikata ɗaya domin inganta aiki da gudanarwa.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ne ya sanar da hakan s cikin wata sanarwa da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da ita.
Sanarwar ta ce
Ma’aikatar za a rika kiranta da “Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi.
Sanarwar ta kara r da cewa wannan na daga cikin kokarin gwamnati na inganta tsarin gudanarwa, da ƙarfafa aiwatar da manufofi, da kuma amfani da albarkatu yadda ya kamata wajen magance matsalolin ruwa da muhalli a fadin jihar kano
Ma’aikatar za ta yi aiki da sassa biyu the wato sashin Albarkatun Ruwa
da sashin Muhalli da Sauyin Yanayi.
Kowane sashin zai kasance karkashin babban sakatare , sannan duka biyun za su kai rahoto kai tsaye ga Kwamishinan ma’aikatar.
Gwamnati ta umurci dukkan sassa da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatun da abin ya shafa da su sauya tsarin aiki da sadarwarsu nan take don daidaita su da sabon tsari.
Matakin ya fara aiki yanzu haka, kuma an bukaci duk masu ruwa da tsaki da su ba da hadin kai domin sauyin ya gudana cikin sauki.
