
Al’ummar garin Dayaso da ke Mazabar Gwangwan a Karamar Hukumar Rogo, Jihar Kano, sun gudanar da taron zumunci domin tattauna matsalolin da suka dade suna addabar al’ummarsu sakamakon rashin kulawar gwamnati a matakai daban- daban.
Taron ya haɗa mazauna garin, shugabannin al’umma, matasa, mata, manoma da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna ƙalubalen da garin ke fuskanta.
Da yake zantawa da Jami’in Yaɗa Labarai na Karamar Hukumar Rogo Abdu Bako Abdullah, bayan kammala taron da aka gudanar a Makarantar Firamare ta Dayaso, Shugaban Ƙungiyar Zumunta Dayaso Malam Adda’u Usman ya bayyana cewa bayan doguwar tattaunawa, mahalarta taron sun gano muhimman matsaloli da ke buƙatar kulawar gwamnati cikin gaggawa.
A cewarsa, manyan matsalolin sun haɗa da rashin ingantattun kayayyakin more rayuwa kamar wutar lantarki wadda aka sanya musu falafalai tsawon shekara bakwai amma babu wayar har kawowa yanzu, lalacewar hanyoyi, rashin magudanan ruwa masu aiki da kuma ƙarancin muhimman abubuwan more rayuwa dake cigaba da hana cigaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar yankin.
Ya kuma bayyana ƙalubalen da ke a fannin ilimi da cigaban matasa, inda ya nuna damuwa kan ƙarancin ƙwararrun malamai duk da cewa garin ya samar da masu shedar digiri da kwararru a fannoni daban-daban. Haka kuma ya nuna damuwa kan ƙarancin ayyukan kiwon lafiya Asibitin yankin yana cikin wani hali sakamakon rashin cibiyoyin lafiya da suka dace da yawan al’ummar yankin.
Dangane da cigaban tattalin arziki, ya koka kan rashin shirye-shiryen gwamnati da ke tallafawa ƙananan sana’o’i da ayyukan noman rani dana damina, waɗanda su ne ginshiƙin tattalin arzikin al’ummar yankin.
Malam Adda’u Usman ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da sake gina Gadar Gwangwan ta hanyar ƙoƙarin Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Ya kuma yi kira ga Sanatan Kano ta Kudu, Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila; Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Rogo, Hon. Abdullahi Sani Rogo, Shugaban Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo; da Kansilan Mazabar Gwangwan da su gaggauta ziyartar garin Dayaso domin ganawa da al’umma kai tsaye domin kawo musu daukin magance matsalolin da aka bayyana. “Ya ƙara da cewa Dayaso gari ne mai zaman lafiya da bin doka, wanda ke da himma wajen cigaba da gina ƙasa.
Ya kara bayyana kwarin gwiwarsa cewa yana rokon shugabannin da abin ya shafa dasu amsa wannan kira cikin kyakkyawar niyya domin cigaban al’umma da kuma Jihar Kano baki ɗaya.
A nasa jawabin, mai unguwar Dayaso, Malam Bello Alhaji Garba, ya jaddada cigaba da goyon bayan al’ummar yankin ga manufofi da tsare-tsaren gwamnati abisa jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf. Haka kuma ya yi kira ga mazauna yankin da su guji sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba, yana mai gargadin cewa lalacewar muhalli na haifar da zaizayar ƙasa da sauran matsalolin muhalli, ciki har da waɗanda suka shafi rushewar Gadar Gwangwan a halin yanzu.
