
Trump ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai ranar Talata, lokacin da aka tambaye shi ko ya kamata Beijing ta shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin.
Sai dai ya ce zai yi maraba da duk wata gudunmawa daga shugaban ƙasar China, Xi Jinping, idan hakan zai taimaka wajen dawo da tsagaita wuta.
Shugaban Amurka Donald Trump
Yace kasar bata buqatar temakon china a yakin da takeyi da iran
Shugaban na Amurka ya kuma yi watsi da fargabar matsin tattalin arziƙi da rikicin ka iya haifarwa, yana mai cewa farashin kaya zai sauka bayan yaƙin ya lafa saboda yawaitar samar da mai.
Rahotanni sun ce rikicin ya fara ne bayan harin da Amurka tare da haɗin gwiwar Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu.
