
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wata mata Khadija Ahmad kan zargin bayar da dakuna ga mutane domin gudanar da badala a Bandirawo City da ke Kano.
Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Malam Auwalu Ado Sheshe, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an Hisbah ƙarƙashin jagorancin Malam Hafizu Garba Adakawa sun gudanar da samame a rukunin gidajen Bandirawo City, inda suka kama Khadija Ahmad mai shekaru 30 daga Karamar Hukumar Rimi ta Jihar Katsina.
Hisbah ta ce Khadija Ahmad ta shaida wa jami’an cewa a wasu lokuta tana bayar da dakuna ga mata domin gudanar da karuwanci, sannan a yayin samamen an kuma samu Ali Abubakar mai shekaru 35 tare da Fatima Abubakar mai shekaru 28 a wani daki.
Sanarwar ta ƙara da cewa mutanen ukun sun roki afuwa tare da alkawarin ba za su sake aikata irin wannan abu ba, kafin daga bisani hukumar ta gurfanar da su a gaban kotu domin ci gaba da shari’a.
