Daga Mutawakkilu Ibrahim Idris
Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani ga Muhammadu Sanusi II kan tambayarsa dangane da ci gaba da karɓar bashi da gwamnatin tarayya ke yi, duk da cire tallafin man fetur.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana cewa bashin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke karɓa ba domin almubazzaranci ba ne, sai dai domin zuba jari a muhimman fannoni na tattalin arziki.
Ya ce gwamnatin na amfani da bashin ne wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da suka haɗa da inganta ababen more rayuwa, ƙarfafa tattalin arziki da kuma samar da guraben ayyukan yi ga ‘yan ƙasa.
Tun da farko dai, Sarkin Kano, wanda tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya ne, ya nuna damuwa a wata hira da News Central TV kan dalilin da ya sa har yanzu ake ci gaba da karɓar bashi bayan cire tallafin mai.
Sanusi ya jaddada cewa akwai buƙatar a yi bayani dalla-dalla ga ‘yan ƙasa kan yadda ake tafiyar da harkokin kuɗaɗen gwamnati, musamman a wannan lokaci da ake ƙoƙarin daidaita tattalin arzikin ƙasa.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta ce matakan da ake ɗauka na cikin tsarin gyaran tattalin arziki da nufin tabbatar da dorewar ci gaba da inganta rayuwar al’umma a nan gaba.
Masu sharhi kan al’amuran tattalin arziki na ganin cewa muhawarar na nuna muhimmancin gaskiya da riƙon amana a tafiyar da dukiyar ƙasa, musamman a lokacin da ake fuskantar ƙalubalen tattalin arziki.

