
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu da Warawa, Muhammad Hassan, ya rasu.
An rawaito cewa ɗan majalisar ya rasu ne a daren Juma’a bayan fama da jinya mai tsawo wadda ta shafe sama da shekara guda.
Ya rasu a wani asibiti da ke Abuja, inda ya bar matan aure uku da ’ya’ya 18.
A cewar wata sanarwa da Muhammad Yaro Daba, Shugaban Barrister Media Promoters, ya fitar, za a gudanar da sallar jana’izar marigayin da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Asabar a gidansa da ke Abuja.
Marigayin har zuwa rasuwarsa yana aiki a matsayin ɗan Majalisar Wakilai ta Najeriya, mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu da Warawa a Jihar Kano.