
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa na Kwamishinan Ma’aikatar Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu nan take.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce an umarci tsohon kwamishinan da ya mika ragamar tafiyar da ma’aikatar ga Daraktan Kasuwanci nan take.
Gwamna Yusuf ya nuna godiyarsa bisa ayyukan da tsohon kwamishinan ya yi a lokacin da yake kan mukaminsa.
Ya kuma yabawa gudunmawar da Sagagi ya bayar wajen ci gaban jihar, musamman a fannonin siyasa, addini, da kuma kanana da matsakaitan sana’o’i.
Gwamnan ya masa fatan alheri a ayyukansa na gaba, tare da jaddada wa al’umma kudurin gwamnatinsa na ci gaba da samar da ingantattun ayyuka da kyakkyawan shugabanci a jihar.
Wannan mataki na daga cikin kokarin sake tsara tsarin gwamnati domin tabbatar da ci gaba mai dorewa da bunkasa tattalin arziki cikin tsari.