Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Business
  • Education
  • Featured
  • Health
  • Politics
  • Sports
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram
Facebook Instagram TikTok
BROWN PIGEON MEDIA
SUBSCRIBE
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    FEDERAL GOVERNMENT SUSPENDS PROPOSED WAEC, NECO REGISTRATION FEE HIKE

    July 13, 2026

    FG: FANNIN MA’ADANAI YA JAWO JARIN DALA BILIYAN 3 CIKIN SHEKARU UKU

    June 18, 2026

    GWAMNATIN TARRAYYA TA MUSANTA SHIRIN SOKE HUKUMAR NBAIS

    June 18, 2026

    DEMOCRACY DAY SPEECH: OUR GENERATION MUST SECURE PROSPERITY 

    June 12, 2026

    Senator Barau Reaffirms ECOWAS Parliament’s Commitment to Regional Unity at Commissioning of New ECOWAS Headquarters

    July 3, 2026

    DA DUMI-DUMI: Starmer ya yi Murabus Daga Mukamin Firaministan Birtaniya

    June 22, 2026

    NETANYAHU YA SHA ALWASHIN HANA IRAN MALLAKAR MAKAMIN NUKILIYA

    June 13, 2026

    Girgizar Ƙasa Mai Ƙarfi Ta Hallaka Mutane a Philippines, Ana Fargabar Tsunami a Wasu Ƙasashe

    June 8, 2026

    WAIYA PLEDGES COLLABORATION WITH EX-COUNCILLORS’ FORUM, NORTH WEST APC WOMEN MEDIA GROUP AS BOTH DECLARE SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA

    August 4, 2026

    Ibrahim Abdullahi Waiya: Leadership Defined by Focus, Vision and Service

    August 4, 2026

    KANO RECORDS REVENUE SURGE AS DIGITAL LAND SYSTEM RAISES MONTHLY EARNINGS TO ₦750 MILLION

    August 3, 2026

    Waiya Reaffirms Kano Government’s Commitment to Community-Led Security, Peacebuilding

    August 3, 2026
  • Business

    KASEDA TA GUDANAR DA SHIRIN WAYAR DA KAI GA MSMEs KAN KA’IDOJIN NAFDAC A JIHAR KATSINA

    June 12, 2026

    Dangote Industrialising Africa– NCCIMA DG

    May 17, 2026

    INEC TA BUKACI MASU RIJISTAR KATIN ZABE A KANO DA SU JE SU DUBA SUNAYENSU

    April 27, 2026

    KANO TO HOST NATIONAL LAUNCH OF ECoN INITIATIVE, SET TO DRIVE INNOVATION AND INDUSTRIAL GROWTH IN NORTH-WEST

    April 16, 2026

    NewsNigeria’s Inflation Rate Climbs to 15.38% in March

    April 16, 2026
  • Education

    KANO PRIVATE SCHOOLS BOARD SUSPENDS 10% STATUTORY TAX PENDING FRESH ASSESSMENT

    August 1, 2026

    2027 PRESIDENCY: TINUBU DECLARES UNIVERSITY DEGREE, LEAVES OUT PRIMARY, SECONDARY EDUCATION

    August 1, 2026

    Governor Abba Kabir Yusuf, Education Minister Commission New Girls’ Secondary School in Kumbotso

    July 22, 2026

    Gwamnatin Kano Ta Umarci Jami’ar Azman Ta Gabatar da Takardun Gini Ko Ta Fuskanci Rufe Makarantar

    June 23, 2026

    Kano Govt Reaffirms Commitment to Children’s Welfare at International Children’s Day Celebration

    June 14, 2026
  • Featured

    Kano State Government Organises Two-Day Retreat for Online Media Publishers in Jigawa

    January 15, 2026

    Former Kano APC Councilors Hold Special Prayers for Governor Abba Kabir Yusuf

    October 27, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    Kano Government Clarifies Position on Elders Council, Backs Its Own Initiative

    September 7, 2025
  • Health

    NORTH-WEST DEVELOPMENT COMMISSION TEAMS UP WITH DALA ORTHOPAEDIC HOSPITAL TO EASE MEDICAL COSTS

    August 1, 2026

    Kano Government Targets Maternal Mortality with 484 New Mini-Ambulances for Rural Wards

    June 19, 2026

    Gwamnatin Kano Ta Sayi Ƙananan Motocin Asibiti 484 Domin Taimaka wa Mata Masu Juna Biyu – Kwamishinan Lafiya

    June 19, 2026

    SHAYAR DA NONON UWA ZALLA NA KARE YARA DAGA CUTUTTUKA — KWAMISHINAN LAFIYA

    June 16, 2026

    Hukumar Kula da Asibitocin Kano Ta Tsaurara Matakai Kan Rashin Zuwa Aiki bisa Jadawalin Ayyuka

    June 11, 2026
  • Politics

    SANATA RUFAI SANI HANGA YA FICE DAGA JAM’IYYAR NDC

    August 3, 2026

    KWANKWASIYYA-SHEKARAU UNITY FORUM REBRANDS, DECLARES TOTAL SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA KABIR YUSUF AHEAD OF 2027

    July 21, 2026

    Governor Abba Kabir Yusuf Declares Murtala Sule Garo as 2027 Deputy Governorship Running Mate

    July 13, 2026

    APC zata Bayyana Shettima a Matsayin Mataimakin Takarar Tinubu na 2027

    July 10, 2026

    TSOFAFFIN SHUGABANNIN ƘANANAN HUKUMOMI DA KANSILOLI SUN BAYYANA GOYON BAYANSU GA GWAMNA ABBA KABIR YUSUF

    July 10, 2026
  • Sports

    Bichi First FC Unveils Abubakar Senior as New Technical Adviser

    September 11, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    If Super Eagles Fail to Qualify for World Cup, Nigerians Will Not Forgive Us – Ahmed Musa

    September 6, 2025

    Super Falcons striker and six-time African Women’s Footballer of the Year, Asisat Oshoala, has completed her move from Bay FC to Saudi Women’s Premier League side Al Hilal

    September 3, 2025
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
BROWN PIGEON MEDIA
Home » DALILIN DA YA SA IKIRARIN GALADIMA A KAN GWAMNA YUSUF YA GAZA TA FUSKAR SAHIHANCI
News

DALILIN DA YA SA IKIRARIN GALADIMA A KAN GWAMNA YUSUF YA GAZA TA FUSKAR SAHIHANCI

Brown Pigeon MediaBy Brown Pigeon MediaMarch 2, 20266 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp Telegram Email Copy Link

DALILIN DA YA SA IKIRARIN GALADIMA A KAN GWAMNA YUSUF YA GAZA TA FUSKAR SAHIHANCI

 

Daga Com. Munir I. Publisher

 

A siyasa, lokaci ba wai kawai yana bayyana dabara ba ne, har ma yakan tona asirin manufa. Lokacin da Alhaji Buba Galadima ya fara hare-hare kan Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano da kuma Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS, hakan bai zo da mamaki ba. Waɗannan hare-haren ba su da tushe balle asali ta fuskar dimokuraɗiyya, sun bayyana ne daidai lokacin da aka cire shi daga kujerar Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, mataki na gudanarwa da aka ɗauka a matsayin wani ɓangare na shirin sake fasalin cibiyoyi da inganta aiki ƙarƙashin Kano First Agenda na Gwamna. Sakamakon wannan jerin abubuwa ba mai wahalar fahimta ba ne: ba batun dimokuraɗiyya ba ne, batun takaici ne.

 

Galadima ya riƙe mukaminsa a Kwalejin ne bisa amincewar gwamna, ba bisa wani haƙƙi na kundin tsarin mulki ba. Irin waɗannan naɗe-naɗe na gwamnati, a tsarinsu, suna ƙarƙashin bita, tantance aiki, da kuma ikon gudanarwa. Shawarar Gwamna Yusuf ta sake fasalin shugabancin Kwalejin, tare da bai wa Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir kujerar shugabanci, amfani ne da wannan ikon domin aiwatar da shirin gyaran cibiyoyi na gwamnati. Babu wani sashe na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, ko Dokar Ilimi (Ƙa’idojin Ƙasa da Kafa Cibiyoyi), ko wata doka da ta bai wa wanda aka naɗa haƙƙin riƙe mukami har abada ko ɗaukar cire shi a matsayin tsanantawa ta siyasa.

 

Salon da Galadima ya bi abu ne da duk wanda ya daɗe yana bibiyar siyasar Nijeriya zai gane nan take. Shiru ko aƙalla rashin sukar gwamnati, lokacin da yake kan mukami. Sai kuma, bayan cire shi, a samu kwatsam an gano “mulkin kama-karya”, “murƙushe ‘yanci”, da “rikicin dimokuraɗiyya” a cikin gwamnatin da lokacin yana kan mukaminsa bai gano hakan ba. Wannan dole akwai abin tambaya a nan.

 

Daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali a ikirarin Galadima akwai yunƙurinsa na jingina Daraktan DSS a Kano da abin da ya kira wani shiri na murƙushe ‘yan adawa. Wannan zargi za a iya kwatanta shi da rashin fahimtar kundin tsarin mulki. DSS hukuma ce ta tarayya da aka kafa ƙarƙashin Dokar Hukumar Tsaro ta Ƙasa ta 1986, tana aiki ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya, kuma tana ba da rahoto ta hannun Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro. ayyukanta ba sa ƙarƙashin umarnin gwamnonin jihohi. Iƙirarin cewa Gwamna Yusuf na ba da umarni ga DSS a Kano kuskure ne mai girma game da yadda tsarin tarayya da tsarin tsaron Nijeriya ke aiki.

 

Daraktan DSS a Kano ya gudanar da ayyukan hukuma cikin hurumin kundin tsarin mulki da kuma bisa sahihan korafe-korafe. Duk inda aka gayyaci wasu domin amsa tambayoyi, an yi hakan ne bisa damuwa mai tushe a ƙarƙashin dokokin Nijeriya, ciki har da Dokar Yaki da Laifukan Yanar Gizo ta 2015, wadda ta fayyace iyakar ‘yancin faɗin albarkacin baki da kuma laifi a sararin yanar gizo. Kiran waɗannan matakai na doka da suna “ramuwar gayya ta siyasa” ba fafutuka ba ce, yin amfani da fahimtar jama’a ne domin manufofi na kashin kai da jam’iyya.

 

Gaskiyar abin da ake gani a Kano ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Yusuf ta saba da labarin Galadima ta kowane bangare. ‘Yan’adawa na magana da aiki cikin ‘yanci. Kafafen yaɗa labarai na gargajiya da na dijital, na aiki ba tare da tsari na takurawa ba. Ayyukan siyasa na gudana a tsakanin jam’iyyu. Ƙungiyoyin farar hula na nan da murya mai ƙarfi. Waɗannan su ne alamomin jiha na gudanar da dimokuraɗiyya ba tare da tawaya ba, amma babu batun murƙushe ‘yanci.

 

A lokaci guda, ayyukan gwamnati suna bayyana kuma suna ƙaruwa. Manyan makarantun gaba da sakandare na Kano na fuskantar gyaran tsarin da aka daɗe ana buƙata. Basussukan gratutoci ga ma’aikatan da suka yi ritaya, waɗanda suka taru tsawon shekaru sakamakon sakaci, ana magance su. Tsarin siyasar ubangida wanda a baya ake raba mukamai a matsayin lada na siyasa maimakon cancanta da muradin jama’a, ana rushe shi sannu a hankali. Tabbas waɗannan sauye-sauye za su jawo rashin jin daɗi ga waɗanda tasirinsu ya dogara da tsohon tsari. Amma rashin jin daɗin masu gata ba rikicin dimokuraɗiyya ba ne. Samun nagartaccen mulki ne.

 

Al’ummar Kano na daga cikin jama’ar da suka fi fahimtar siyasa da tarihi a Nijeriya. Sun sha ganin sauye-sauyen siyasa masu sarkakiya, sun ga ire-iren wannan siyasar ƙorafi da ake gani a yanzu, kuma sun kware wajen bambance sukar dimokuraɗiyya ta gaskiya da kuma takaicin da aka sake masa suna da “fafutuka”. Wannan hikima ya kamata a yi amfani da ita a yanzu, ba tare da son zuciya ba.

 

‘Yancin faɗin albarkacin baki, kamar yadda Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulki ya tanada, haƙƙi ne da wannan gwamnati ba ta taɓa tauyewa ba. Amma abin da ta yi, kuma za ta ci gaba da yi, shi ne tabbatar da cewa ‘yancin magana ba ya rikidewa zuwa “haƙƙin” yaɗa ƙarya, tayar da rikici, ko gina labaran tsanantawa da ba su da tushe. ‘Yancin magana tabbaci ne na kundin tsarin mulki. ‘Yancin ɓatar da jama’a ba haka ba ne. Wannan bambanci ba takura wa dimokuraɗiyya ba ne; sharadi ne na rayuwarta.

 

An zaɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf ne domin ya yi wa al’ummar Kano hidima, ya gyara cibiyoyinta, ya ƙarfafa tsarin mulki, ya kuma gina makoma da ta shafi ‘yanƙasa, ba cibiyoyin rabon gata na siyasar baya ba. Gwamnatinsa na ci gaba da wannan aiki ba tare da shagaltuwa da hayaniyar masu rikita takaicin kansu da manufar dimokuraɗiyya ba.

 

Tarihi, kamar yadda yake yi a kowane lokaci, zai zana layi mai tsabta tsakanin waɗanda suka yi amfani da mukamansu wajen gina cibiyoyi da yi wa jama’a hidima, da waɗanda suka juya zuwa kai hari ga cibiyoyin nan da zarar an cire su daga mukamansu. Kano na buƙatar siyasa mai zurfi, mai tushe a kan manufa, hujja, da muradin jama’a. Abin da Galadima ke gabatarwa babu ɗaya daga cikin waɗannan. Kuma al’ummar Kano masu ilimi da balagar siyasa, sun san bambanci.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email VKontakte WhatsApp Copy Link
Previous ArticleDaukaka Ta Allah Ce: Hakikanin Gwagwarmayar Siyasa da Sakamakonta
Next Article ZARGE-ZARGEN GALADIMA GA GWAMNA YUSUF DA DSS: NA SIYASA NE, BA SU DA HUJJA, KUMA NA IYA JAWO BARAZANA GA TSARIN HUKUMA

Related Posts

WAIYA PLEDGES COLLABORATION WITH EX-COUNCILLORS’ FORUM, NORTH WEST APC WOMEN MEDIA GROUP AS BOTH DECLARE SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA

August 4, 2026

Ibrahim Abdullahi Waiya: Leadership Defined by Focus, Vision and Service

August 4, 2026

KANO RECORDS REVENUE SURGE AS DIGITAL LAND SYSTEM RAISES MONTHLY EARNINGS TO ₦750 MILLION

August 3, 2026

Waiya Reaffirms Kano Government’s Commitment to Community-Led Security, Peacebuilding

August 3, 2026

WAIYA YA JADDADA MUHIMMANCIN HAƊIN GWIWA TSAKANIN AL’UMMA DA GWAMNATI WAJEN INGANTA TSARO A JIHAR KANO

August 3, 2026

Kosan Waka Dies at 47 as Gov. Yusuf Mourns Renowned Political Singer

August 2, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Stay In Touch
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • Telegram
  • WhatsApp
Latest Posts

WAIYA PLEDGES COLLABORATION WITH EX-COUNCILLORS’ FORUM, NORTH WEST APC WOMEN MEDIA GROUP AS BOTH DECLARE SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA

By Brown Pigeon MediaAugust 4, 2026

The Kano State Commissioner of Information and Internal Affairs, Comrade Ibrahim Abdullahi…

Ibrahim Abdullahi Waiya: Leadership Defined by Focus, Vision and Service

August 4, 2026

KANO RECORDS REVENUE SURGE AS DIGITAL LAND SYSTEM RAISES MONTHLY EARNINGS TO ₦750 MILLION

August 3, 2026

SANATA RUFAI SANI HANGA YA FICE DAGA JAM’IYYAR NDC

August 3, 2026

Waiya Reaffirms Kano Government’s Commitment to Community-Led Security, Peacebuilding

August 3, 2026
© 2026 Brown Pigeon Media. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.