
Hukumar gudanarwar Makarantar Legal Studies da ke Kano ta kai ziyarar aiki ga Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban makarantar da kalubalen da take fuskanta.
Shugaban rikon makarantar, Dakta Ali Tamasi Mu’azu, wanda ya jagoranci tawagar, ya bayyana cewa ziyarar na daga cikin kokarin hukumar na neman hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano wajen inganta harkokin makarantar da samar da ingantaccen yanayi ga dalibai da ma’aikata.
Dakta Mu’azu ya gabatar da bayanai kan manya da kananan matsalolin da makarantar ke fuskanta, wadanda suka hada da bukatun more rayuwa, kayan aiki da sauran abubuwan da ake bukata domin inganta harkokin karatu da gudanar da ayyukan makarantar yadda ya kamata.
Ya ce Makarantar Legal Studies na taka muhimmiyar rawa wajen horar da dalibai da za su kasance kwararru a fannin shari’a, don haka akwai bukatar kara ba makarantar kulawa domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Shugaban rikon ya kara da cewa magance matsalolin makarantar zai taimaka wajen bunkasa harkar ilimi da samar da kwararrun ma’aikata a bangaren shari’a, tare da bai wa dalibai damar samun ingantaccen ilimi da horo.
A nasa bangaren, Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya saurari bayanan da hukumar ta gabatar, tare da nuna muhimmancin ziyarar wajen fahimtar halin da makarantar ke ciki.
Ya yaba da kokarin hukumar wajen neman hanyoyin inganta harkokin makarantar, yana mai jaddada muhimmancin hada kai tsakanin hukumomin ilimi da gwamnatin jihar domin samun ci gaba mai dorewa a fannin ilimi.
