
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da inganta harkokin tsaro tare da samar da tsare-tsaren, hukumomi da kungiyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma a fadin jihar.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin wani taron karramawa da Institute of Security and Strategic Studies (ISSS) ta shirya, inda ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa tsaro a yankin Arewa maso Yamma da kasa baki daya.
Kano first

A cewar kwamishinan, gwamnatin Kano na ci gaba da daukar matakai masu dorewa domin karfafa tsaro, tare da hada kai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen magance matsalolin rashin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Da yake jawabi bayan gabatar da lambar yabo, Shugaban Hukumar Institute of Security and Strategic Studies, Dakta Henry Onwokoji Chiedozie, ya bayyana cewa an zabo Gwamna Abba Kabir Yusuf ne don karramawar sakamakon irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa zaman lafiya da tsaro.
Dakta Chiedozie ya kuma yabawa shirin Safe Corridor, wanda Kwamishina Ibrahim Waiya ke jagoranta karkashin kulawar gwamnatin Kano, musamman bangaren Tudun Muntsira, wanda ke mayar da hankali wajen gyaran tarbiyyar matasa musamman dawo da masu shaye-shaye da masu tayar da hankali cikin al’umma zuwa hanya madaidaiciya.
Ya ce irin wadannan shirye-shirye na tsamo matasa ta hanyar tsarin tudun mun tsira da wayar da kai kan fadace-fadace na taka muhimmiyar rawa wajen rage laifuka da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Kano.
