
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce duk wanda zai ci gajiyar shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shirin gudanarwa, ba zai iya raba auren ba sai bayan ya dawo hukumar domin sasanta duk wata matsala da ta taso a tsakaninsu.
Babban Kwamandan Hukumar na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a wani ɓangare na fara shirin auren gata na mutane 3,000 da gwamnatin jihar ke shirin aiwatarwa.
Sheikh Daurawa ya ce gwamnatin jihar ta kashe kuɗi masu yawa wajen tallafawa ma’auratan domin ganin an samu zaman lafiya da dorewar aure, don haka duk wanda yake son rabuwa da matarsa saboda wata matsala ya zama wajibi ya gabatar da korafin ga hukumar Hizba.
Ya kara da cewa gwamnatin Jihar Kano ta ware kuɗi Naira biliyan ɗaya da rabi domin gudanar da shirin wanda zai amfanar da ma’aurata 3,000 a faɗin jihar.
Kano first

Daurawa yace shirin auren zai haɗa da samar da kayan ɗaki da da kayan abinci da kuma tallafin kuɗi domin rage wa marasa galihu wahalhalun da ke tattare da yin aure.
Hukumar Hisbah ta kuma yi kira ga ma’auratan da za su ci gajiyar shirin da su riƙe aurensu da muhimmanci tare da kasancewa masu haƙuri da juna musamman idan matsala ta taso.
Brown Pigeon Media ta ruwaito sheikh Daurawa na jaddada manufar shirin na taimakawa matasa da marasa galihu wajen yin aure tare da gina iyalai masu albarka.
