
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.
Sauran jam’iyyun da kotun ta bayar da umarnin cire rajistarsu sun haɗa da APP, AA, AP da kuma ZLP. Alƙali Peter Lifu ne ya yanke wannan hukunci.
Kano first

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Ƙungiyar Tsoffin ‘Yan Majalisu ta Ƙasa (National Forum of Former Legislators) ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026, inda ta nemi kotun ta fayyace ko INEC na da ikon doka da kundin tsarin mulki na cire rajistar jam’iyyun siyasa da suka gaza cika sharuddan da ke cikin Sashe na 225A na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), tare da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2022 da ka’idojin INEC.
Kotun ta tabbatar da cewa INEC na da alhakin aiwatar da tanade-tanaden doka kan jam’iyyun siyasa da suka gaza bin ka’idojin da kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe suka gindaya.
