
Za mu maka Kwankwaso a kotu bisa siye fom din yan takarar PRP na Kano su 69 – Masu ruwa da tsaki
Masu Ruwa da Tsaki na Jam’iyyar PRP na shiyyar Arewa maso Yamma sun zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da saye fama-faman yan takarar jam’iyyar na Kano, lamarin da suka ce zai iya hana mambobin da suka cancanta damar tsayawa takara.
Shugaban kungiyar masu ruwa da tsakin, Abdulkadir Musa Guza ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano a yau Lahadi.

Ya ce jam’iyyar na zargin Kwankwaso da saye fom ɗin takara na dukkan matakai 69 na jam’iyyar PRP, inda ya zargi tsohon gwamnan da zagon kasa bayan shi ba dan jam’iyyar ba ne.
Guza ya bayyana damuwa ga makomar dimokuraɗiyya da tsarin gudanar da harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa.
A cewarsa, matakin zai iya hana mambobin jam’iyyar da suka cancanta kuma suke da niyyar tsayawa takara damar samun tikitin jam’iyyarsu.
Ya bayyana lamarin a matsayin “fashin siyasa” wanda zai iya haifar da rikice-rikice da ruɗani a harkokin zaɓe idan ba a dakatar da shi ba.
Guza ya jaddada cewa PRP jam’iyya ce mai bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya kuma ba za ta amince da duk wani yunƙuri na kwace ikon tafiyar da harkokinta ba.
Ya yi kira ga Kwankwaso da ya bar jam’iyyun siyasa su gudanar da harkokinsu cikin ‘yanci da adalci, yana mai cewa bai kamata a tsoma baki cikin harkokin PRP ba.
Shugaban dandalin ya kuma yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da abin da ya kira katsalandan a harkokin jam’iyyar, za su nemi mafita ta hanyar kotu domin kare haƙƙin mambobinsu da martabar jam’iyyar.
DN/RAM
