
Daga Brown Pigeon Media
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da sayen ƙananan motocin asibiti guda 484 domin inganta ayyukan kiwon lafiya da kuma sauƙaƙa jigilar marasa lafiya, musamman mata masu juna biyu, zuwa cibiyoyin lafiya a faɗin jihar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka shirya domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya da kuma cika shekaru uku na mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya bayyana cewa za a raba motocin ga dukkan mazabu 484 da ke cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda za su taimaka wajen kai marasa lafiya daga yankunan karkara zuwa asibitoci cikin gaggawa.
A cewarsa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage mace-macen mata masu haihuwa da jarirai tare da ƙara samun damar kula da lafiyar al’umma a matakin farko.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta ninka kasafin kuɗin shirin kula da mata masu juna biyu daga Naira miliyan 30 zuwa miliyan 60 a kowane wata domin ƙara yawan mata da za su amfana da shirin.

Haka zalika, ya ce gwamnati na shirin ɗaga matsayin manyan asibitoci shida zuwa asibitocin ƙwararru a yankuna shida na jihar, domin kusantar da ayyukan kiwon lafiya na musamman ga al’umma.
Dangane da samar da magunguna, Labaran Yusuf ya ce asibitocin da ke aiki da tsarin Drug Revolving Fund (DRF) sun samu gagarumin ci gaba, inda yawan magungunan da ake samu ya ƙaru daga kashi 30 cikin 100 a shekarar 2023 zuwa kashi 96 cikin 100 a halin yanzu.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu nasarar cika kusan kashi 95 cikin 100 na alƙawurran da ta ɗauka a fannin kiwon lafiya cikin shekaru uku da suka gabata.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da saka hannun jari a fannin kiwon lafiya domin tabbatar da ingantaccen kulawa ga al’ummar Kano.
