
Kwamitin wayar da kan jama’a kan muhimmancin yin katin zabe da gwamnatin jihar Kano ta kafa a shekarar 2025, yayi zama da wakilan kwamitin domin tattauna yadda ake gudanar da rijistar katin zaben a sassa daban- daban na jihar kano .
Shugaban kwamitin wayar da kan jama’a ga me da yin rijistar katin zaben, kana kuma Kwamishina yada labarai da al’amurran cikin gida na jihar Kano kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin wani zama na musamman da kwamitin yayi haɗin gwaiwa da wakilan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC domin tattauna ci gaban da aka samu wajen gudanar da rijistar katin zaben.
Kano first

Waiya yace hakika nasarar hakan ta samu ne sakamakon yadda mai girma gwamna Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada gudunmawa da tallafi wajen kafa kwamitin da yayi namijin kokari wajen wayar da kan al’umma musamman matasa da basu taba yin katin zabe ba.
Yace nasarar da jihar Kano ta samu har ta kai ta zamo kan gaba wajen yawan masu yin rijistar katin ba wai iya rijistar a yanar gizo bane hadda sauran duk wasu matakai da ake bi na kammala rijistar katin zaben da jama’a suka bi yasa Kano ta zama ta farko.
Ya kara da cewa bangaren mutanen karkara da rugagen Fulani ma gwamnati ta dauki mata kai da zasu taimaka wajen ganin an saukaka musu yadda zasu mallaki katin zaben, inda ma’aikatar yada labarai ta tura jami’an ta wajen ganin an zakulo hanyoyi da gudummawar da shugabannin kananan hukumomi zasu bayar wajen tabbatar da duk wani rukunin al’umma sun shiga tsarin mallakar katin zaben cikin sauƙi.
Daga nan Kwamishina Waiya ya godewa Al’umma bisa hadin kai da suke bayarwa wajen karbar wayar da kan da ake yi ta kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta har aka kai ga cimma wannan Nasarar.
COV/ RAM.
