Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da bayar da tallafin naira miliyan 265 ga alhazan bana su 3,620 daga jihar domin taimaka musu da bukatunsu na yau da kullum yayin gudanar da aikin Hajji a ƙasar Saudiyya.
Rahotanni sun ce kowane mahajjaci zai karɓi Riyal 200 a matsayin tallafi daga gwamnatin jihar.
An bayyana cewa tallafin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin rage wa maniyyata wahalhalu tare da inganta jin daɗinsu a yayin gudanar da ibadar Hajji.
Haka kuma gwamnatin ta ce za ta ci gaba da samar da duk wata kulawa da tallafin da ya dace domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana ga alhazan jihar Kano.

