
Hukumar Kwastam ta kasa ta ce ta kama haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai Naira miliyan 273.6 a wani sabon samame da ta gudanar a jihar Cross River.
Kwanturolan Hukumar na yankin, Mista Momodu Dauda, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Laraba, inda ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da aiwatar da manufofin haraji na gwamnati tare da kare tattalin arzikin ƙasa.
A cewarsa, jami’an Kwastam sun kama wata babbar mota a ranar 14 ga Yunin 2026 a kan hanyar Odukpani zuwa Calabar, ɗauke da kwantena biyu cike da man girki da aka shigo da shi daga ƙasashen waje.

Ya ƙara da cewa hukumar ta kuma kwace tsofaffin tayoyi guda 1,500 da darajarsu ta kai Naira miliyan 61.3, tare da manyan buhunan tufafin gwanjo guda 105 da aka kiyasta darajarsu ta kai Naira miliyan 15.6.
Dauda ya ce jami’an sun kuma kama lita 800 na man fetur da darajarsa ta haura Naira miliyan ɗaya, yana mai cewa an lalata man fetur ɗin
Ya jaddada cewa dukkan kayayyakin da aka kama suna cikin jerin kayayyakin da Gwamnatin Tarayya ta haramta shigowa da su ƙasar nan yace
matakin ya yi daidai da tanadin Sashe na 55 na Dokar Hukumar Kwastam ta Najeriya ta shekarar 2023.
A cewarsa, jimillar darajar kayayyakin da aka kama ta kai Naira miliyan 273,676,021, tare da gargadin masu safarar haramtattun kayayyaki da su daina wannan sana’a.
Haka kuma, ya yaba wa Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, bisa ƙoƙarinsa na ƙarfafa ayyukan sa ido da inganta yadda hukumar ke gudanar da aikinta a faɗin ƙasar nan.
