
Hukumar Hizba ta Jihar Kano ta kai samame wani otel da ke yankin Yahaya Gusau, Buk Road da Danbare, a ƙarƙashin shirin “Operation Kau da Badala”, inda ta samu nasarar kama wasu da ake zargi da aikata laifukan da suka saɓa wa dokokin hukumar, biyo bayan korafe-korafen da al’umma suka gabatar.
Da yake jawabi ga manema labarai Mataimakin Kwamandan Hukumar Hizba ta Jihar Kano, Sheikh Mujahiddin Aminuddeen, ya ce hukumar ta kama maza shida da mata goma a yayin samamen. Ya ƙara da cewa an ladabtar da su, kuma za’a mikasu ga iyayensu tare da sharudda
