
Masarautar kasar Saudiyya ta fara rabon Alƙur’ani Mai Tsarki miliyan 1.9 dake dauke da fassarorinsa cikin harsuna sama da 80 ga Alhazan da suka kammala aikin Hajjin bana, a matsayin kyauta ta musamman yayin da suke komawa ƙasashensu.
Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci,da Da’awa da Shiryarwa ta Saudiyya ta bayyana cewa an gudanar da rabon ne a filayen jiragen sama, mashigai na kan iyakoki da tashoshin jiragen ruwa domin tabbatar da cewa Alhazai daga sassa daban-daban na duniya sun karɓi wannan kyauta kafin barin ƙasar.
A cewar ma’aikatar, an fassara kwafen Alƙur’anin zuwa harsuna fiye da 80, domin bai wa Musulmai daga ƙasashe daban-daban damar fahimtar ma’anonin Alƙur’ani cikin yarukan da suka fi amfani da su.
Mahukuntan Saudiyya sun ce wannan shiri na daga cikin manyan ayyukan da Masarautar ke aiwatarwa don yaɗa saƙon Alƙur’ani Mai Tsarki a faɗin duniya, tare da ƙarfafa alaƙar ruhaniya da Alhazai bayan kammala ɗaya daga cikin manyan rukunnan Musulunci.
Sun ƙara da cewa rabon Alƙur’anin ya zo ne a matsayin wani ɓangare na hidimomin da Saudiyya ke ci gaba da samarwa ga baƙin Allah, tun daga lokacin isowarsu ƙasar har zuwa lokacin da suke komawa gida bayan kammala ibadunsu.
Alhazai da dama sun bayyana jin daɗinsu kan wannan kyauta, suna mai cewa za ta kasance abin tunawa mai ɗorewa ga tafiyar Hajjin da suka gudanar, tare da taimaka musu wajen ci gaba da karanta Alƙur’ani da fahimtar koyarwarsa bayan dawowarsu gida.
Wannan mataki ya sake nuna irin kulawa da muhimmancin da Masarautar Saudiyya ke bai wa hidimtawa Alƙur’ani Mai Tsarki da kuma miliyoyin Musulman da ke ziyartar ƙasar domin gudanar da aikin Hajji a kowace shekara.
