
Wani sabon rahoto da cibiyar bincike ta SBM Intelligence ta fitar ya bayyana Kano State a matsayin jiha mafi dacewa da zaman iyalai a Najeriya.
Rahoton, wanda ya samo asali daga binciken da aka gudanar tsakanin watan Afrilu da Mayun 2026, ya tattara ra’ayoyin mutane 442 daga jihohi daban-daban na ƙasar nan. Binciken ya mayar da hankali ne kan muhimman fannoni da suka haɗa da tsaro, arahar rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, kula da yara, samar da wutar lantarki da kuma irin tallafin da al’umma ke bai wa juna.
Sakamakon binciken ya nuna cewa Kano ce ta fi kowace jiha samun maki mafi girma, musamman a fannonin tsaro, kula da yara, arahar rayuwa da kuma samar da wutar lantarki. Rahoton ya kuma bayyana cewa sama da kashi 80 cikin 100 na waɗanda suka halarci binciken sun nuna gamsuwa da matakin tsaro a yankunansu.
A cewar SBM Intelligence, nasarar Kano ta samo asali ne daga ƙarancin tsadar rayuwa, ƙaƙƙarfan tsarin zamantakewa, da kuma haɗin kai da tallafin da iyalai da al’umma ke bai wa juna, abubuwan da suka taimaka wajen samar da yanayi mai kyau ga rayuwar iyalai.
Rahoton ya ƙara da cewa akwai darussa masu muhimmanci da sauran jihohin Najeriya za su iya koya daga tsarin zamantakewa da dabarun da Kano ke amfani da su wajen inganta walwala da rayuwar al’umma.
Masana na ganin wannan matsayi da Kano ta samu wata alama ce ta ci gaba a kokarin samar da yanayin rayuwa mai inganci da kwanciyar hankali ga mazauna jihar.
