
Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana cewa alhazanta 2,090 sun kammala aikin Hajjin bana cikin nasara ba tare da wata babbar matsala ba. Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar, Dr. Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya ce mafi yawan alhazan sun kammala jifa da zaman kwanaki biyu a Minna, yayin da sauran ke kammala zaman kwana na uku.
Ya tabbatar da cewa ba a samu wata matsala da ta shafi katin Nusuk ko lafiyar alhazai ba. Sai dai ya sanar da rasuwar Alhaji Shehu Yahaya Jalam, daya daga cikin jagororin alhazan jihar, bayan isowarsa Makkah. Haka kuma ya yaba da gudunmawar jami’ai da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.
