
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina State ta ƙaddamar da wani sashe na musamman mai suna Violent Crime Response Unit (VCRU), domin ƙara ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro da suka haɗa da garkuwa da mutane, fashi da makami, ta’addancin ’yan bindiga, satar shanu da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Yayin ƙaddamar da sabon shirin a ranar Juma’a, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ali Umar Fage ya bayyana cewa an kafa VCRU ne bisa tsarin gyare-gyare da manufofin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu domin inganta ƙwarewa, gaskiya da kuma aikin rundunar ’yan sanda.
A cewarsa, sabon sashen zai haɗa ayyukan rundunonin musamman daban-daban a ƙarƙashin tsari guda mai amfani da bayanan sirri domin dakile duk wata barazanar tsaro cikin gaggawa.
Ya ƙara da cewa kafa wannan sashe ya zo ne a daidai lokacin da ake matuƙar buƙatarsa, musamman duba da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihar da ma Arewa baki ɗaya.
Kwamishinan ya bayyana fatan cewa sabon tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro a jihar tare da ƙara samun amincewar jama’a ga ayyukan rundunar ’yan sanda.
Masu lura da al’amuran tsaro na ganin cewa ƙaddamar da VCRU na daga cikin matakan da hukumomin tsaro ke ɗauka domin inganta martani cikin gaggawa ga manyan laifuka da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
