
By Sadiya Tsoho Salisu Kosawa
A dede lokacin da damuna tayi nisa a wasu jihohin Kasar nan gwamnatin jihar kano ta shawarci Al’umma da su cigaba da gyaran maguda nan ruwa da kwashe Shara kawar da datti domin kaucewa ambaliyar ruwa
Kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi na jihar kano Dr Dahiru Muhammad Hashim ne yayi wannan Kira a talatar nan yayin dayake tattaunawa da brown pigeon media a ofishinsa
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin kano tayi tanadi na Kayan aikin tsaftar muhalli da yashe maguda nan ruwa domin tunkarar damunar bana
Yayi Kira ga matasa dasu cigaba da alkinta dashen da gwamnatin kano tayi domin amfanin Al’ummar kano baki daya
