
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, a ranar Alhamis ya wakilci Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a taron Women in Security Summit (WINSEC) na shekarar 2026, wanda Ƙungiyar ‘Yan Jarida Mata ta Ƙasa (NAWOJ) ta shirya a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja.
A yayin taron, Comrade Waiya ya karɓi lambar yabo ta WINSEC Award of Excellence a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, saboda ƙwarewarsa da bajintarsa wajen shugabanci na musamman a fannonin zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci.
Da yake jawabi bayan karɓar lambar yabon, Waiya ya bayyana kyautar a matsayin wata shaida da ke nuna irin kyakkyawan shugabanci da Gwamna Yusuf ke yi, da kuma salon mulkin da ya mayar da jin daɗin al’umma a matsayin babban abin da ya fi mayar da hankali a kai. Ya ce gwamnatin na nan daram wajen tabbatar da samar da ingantaccen aiki da hidima ga al’ummar Jihar Kano.
Ya kuma miƙa godiyarsa ga waɗanda suka shirya taron a madadin Gwamnan, gwamnati da al’ummar Jihar Kano, yana mai cewa wannan karramawa za ta ƙara wa gwamnatin ƙwarin gwiwar ci gaba da riƙe amana, nagarta, ƙwarewa da kuma bin ƙa’idojin gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da aikin gwamnati.
Waiya ya taya Gwamna Yusuf murnar wannan karramawa da ya ce ya cancanta, yana mai danganta nasarar da kyautar da irin hangen nesan shugabancin Gwamnan, wanda ya ce yana ci gaba da ƙarfafa jami’an gwamnati wajen bayar da gudunmawarsu mafi inganci domin ci gaban jihar.
Baya ga karɓar lambar yabon Gwamna, Comrade Waiya shi ma NAWOJ ta karrama shi da lambar yabo ta Award of Excellence in Strategic Communication, saboda gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta sadarwar jama’a da gudanar da harkokin yaɗa bayanai cikin tsari da dabaru.
Ya gode wa ƙungiyar NAWOJ bisa waɗannan karramawa guda biyu, yana mai bayyana lambobin yabon a matsayin babbar girmamawa da kuma ƙarin nauyin da zai ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da inganta shugabanci nagari da sadarwa mai ma’ana domin amfanin al’ummar jihar.
Kwamishinan ya kammala jawabinsa da gode wa Allah Maɗaukakin Sarki, yana mai cewa dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa wannan babban karamci da aka yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da shi kansa.
